Tarihi Da Waƙoƙin Uwani Zakirai

6,000.00

Hajiya Salamatu Uwani Zakirai (1933-1998) ta ciri tuta a fagen waƙar baka da waƙoƙin madahu marasa kiɗa. Duk da ɗimbin waƙoƙin da ta yi kan jigogi daban-daban, an fi sanin ta da waƙar soyayya ta ‘Azizu Ɗan Makaranta’. Uwani ce zabiya ta farko da aka ɗauki waƙar ta a gidan Rediyo Talbijin Kaduna lokacin da aka buɗe tashar a cikin 1962; mace ta farko da ta yi waƙoƙin addini a gidan rediyon, kuma Bahaushiya ta farko da aka ɗauka a gidan rediyo tana amfani da kayan kiɗa guda biyu a lokuta mabambanta, wato kalangu da kukuma. Bayan ta yi aure sai ta yi ritaya daga harkar waƙa, ta sadaukar da kan ta ga kyautata rayuwar iyalin ta da sauran jama’a har ta koma ga Mahalicci.

A cewar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya na Jami’ar Jihar Sakkwato: “‘Tarihi Da Waƙoƙin Uwani Zakirai’ littafi ne da ya cancanta kowaɗanne ɗaliban manyan makarantu su naƙalce shi domin ilmin da ya tara, kama daga abubuwan da suka danganci babban saƙon sa da ya ƙunsa har zuwa ga dabarun aiwatar da bincike da gabatar da sakamakon bincike. Haƙiƙa Ibrahim Sheme ya taskace mana tarihi da ayyukan ɗaya daga cikin mawaƙan baka na Hausa da ke neman su salwanta. Allah ya albarkaci wannan aiki, amin.”

Category: Tags: , , ,