Alhaji Mamman Shata Katsina shi ne mawaƙin baka mafi shahara a ƙasar Hausa. Ya shafe sama da shekara sittin ya na sana’ar roƙo. Kuma ya ciri tura a wasu fannonin, kamar noma, kiwo, kasuwanci, da siyasa.
Dubban waƙoƙin sa ma’auni ne na rayuwar Hausawa da na Afrika a zamanin sa. Cike su ke da hikima, kuma su na da ɗimbin tasiri a al’umma.
Wannan littafi ya na ƙunshe da ƙarin haske kan wanene Shata da ruƙuƙin da ya ratsa a rayuwar sa, da wasu sassa na rayuwa a ƙasar Hausa kamar yadda za a gani a tarihin shi da na ɗimbin mutanen da ya yi wa waƙa ko ya shafi rayuwar su.
Reviews
There are no reviews yet.